Falasdinawa biyar sun halaka a yankin Gaza
April 6, 2018Talla
Falasdinawan dai sun kunna wa tayoyi wuta da zummar tada hayaki da zai baddala hangen nesan sojojin na Isra'ila masu harbi daga nesa.
Kisan na wannan Juma'a dai ya sanya adadin Falasdinawan da aka halaka sun kai 27. Ma'aikatar lafiya a yankin na Gaza ta bayyana cewa akwai mutane 1,070 da suka samu raunika a yayin zanga-zangar ta wannan rana, cikinsu akwai mutane 25 da suka samu munanan raunika har da mata 25 da kananan yara 48.
Jagororin Hamas dai sun bayyana cewa za a dauki tsawon makonni ana wannan zanga-zanga don ganin Isra'ila ta kauce daga killace iyakar da take yi a yankin, yayin da daga bangaren na Isra'ila ke cewa masu zanga-zangar na son fakewa da wannan ne don kai hare-hare.