1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Falasdinawa na ci gaba da gwagwarmaya

January 5, 2015

Bayan da aka yi watsi da bukatarsu a gaban Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, mahukuntan Falasdinawa sun ce za su sake mika bukatar neman kawo karshen mamayar da Isra'ila ke musu.

Hoto: picture-alliance/epa/Peter Foley

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya ce za su sake mika daftarin bukatarsu ta neman Isra'ila ta kawo karshen mamayar da take musu nan da shekaru uku masu zuwa a gaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. A makon da ya gabata dai Falasdinawan sun mika daftarin gaban Kwamitin Sulhun, sai dai bai samu nasarar wucewa ba biyo bayan gaza samun kuri'un kasashe taran da ake bukata daga cikin kasashe 15 mambobin Kwamitin. Kasashe takwas ne suka kada kuri'ar amincewa yayin da Amirka da Ostareliya suka hau kujerar na ki. Kashe biyar sun kaurace wa kada kuri'a ciki kuwa har da Birtaniya. Mahukuntan na Falasdinu dai sun nuna damuwarsu dangane da kunyar da suka ce Najeriya ta basu ta hanyar saba alkawarin da ta yi bayan da ita ma ta kaurace wa kada kuri'a, abunda suka ce a baya ta yi alkawarin kada kuri'ar amincewa. Mahukuntan na Falasdinu dai sun danganta matakin na Najeriya da matsin lamba daga Amirka ko kuma Amirkan ta yi wa Najeriyar wasu alkawarurruka.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal