1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Falasdinawa sun cimma yarjejeniyar sulhu

Mahmud Yaya Azare RGB
October 14, 2022

Kungiyoyin Falalsdinawa na Al-Fatah da Hamas da suka jima suna zaman 'yan marina, sun yi nasarar cimma yarjejeniyar sulhu da za ta kai ga shirya zabe.

Falasdinawa sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya
Hoto: Fazil Abd Erahim /AA/picture alliance

Manyan kungiyoyin Falalsdinawa Al-Fatah da Hamas, da suka jima suna zaman 'yan marina, sun yi nasarar cimma yarjejeniyar sulhun da za ta kai ga shirya zabe cikin tsukin shekara guda, albarkacin shiga tsakanin da shugaban kasar Aljeriya Abdulmajeed Tabboun ya yi a birnin Aljez na kasar ta Aljeriya. 

Bayan kwashe shekaru 15 ba sa ga maciji da juna da yakai ga raba iko Falalsdinawan tsakanin gwamnatoci biyu, daya a Ramallah daya a  Zirin Gaza, daga karshe Shugaba Abdulmajeed Tabboun, ya yi nasarar hada kansu don cimma yarjejeniyar dunkulewa su zama tsintsiya madaurinki daya. 

 Masharhanta dai sun yi amanar cewa, shugaban na Aljeriya,wanda kasarsa a shekarun baya ta yi nasarar shirya taron da Yasir Arafat ya ayyana kafuwar kasar Falalsdinu shekaru kusan 40 din da suka gabata, a yanzu shugaban na Aljeriya yana son farfado da irin wannan tasirin da kasarsa ke da shi ne, musamma bayan da babbar abokiyar hamayyarsa kuma makwabciyarsa kasar Maroko ta kulla hulda da Isra'ila. 

Falasdinawa a yayin bikin yaye daliban jami'aHoto: Yaser qudih/ZUMAPRESS.com/picture alliance

 Ana dai Fargabar cewa, kasar Masar wace ke makwabtaka da Falalsdinu wace kuma ta sha gwabza yaki da Isra'ila har kusan sau uku don kwato hakkokin Larabawa, kasar ta Masar ba za ta yarda da Aljeriya tai mata dan waken zagaye a batun da a shekarun bayan nan take daf da karkareshi ba. 

To koma dai ya lamarin zai kaya, al'umomin Falalsdinu da ke cewa sun jima sana musu gafara sa dangane da batun yin sulhun ,amma ba su ga ko kaho ba, saboda haka duk da alkawuran da jagororin Falalsdinawa su ka yi ta yi a yayin taron na Aljeriya suke cewa, mu gani a kasa ance da kare ana suna a gidanku. 

Falasdinawa sun cimma yarjejeniyar sulhu Hoto: picture-alliance/dpa/M. Saber

Wani gamo da Katar da Falasdinawa suka yi,shi ne, a daidai lokacin da Falasdinawan ke cimma wannan sulhun a Aljeriya sai ga shi Isra'ila na sanar da sassauta musu takunkumin zirga-zirga da huldar kasuwanci da shi ne mafi girma cikin shekarun da suka yi karkashin killacewa da takunkuminta. 

Sashen ayyukan Gwamnati a Yankunan Falasdinawa (COGAT) ya shaida cewa, Isra'ila ta bayar da  izinin kamun kifi ga masuntan Zirin Gaza a nisan mil 15 a teku maimakon mil 12. Ta kuma bude kofar Karm Abu Salim da ke kan iyaka domin shiga da fitar da kayayyaki gami da bai wa 'yan kasuwar Gaza dubu biyar izinin shiga Isra'ila don kasuwanci, haka zalika za,a kara yawan ruwan shan da ake aika wa Gaza daga Isra'ila. 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani