1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila za ta yi amfani da iko don karin gabar kogin Yamma

Zulaiha Abubakar MNA
September 10, 2019

Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya baiyana shirin amfani da karfin ikon kasar wajen shigar ya mashigin ruwan Jordan cikin gabar kogin Yammacin kasar idan ya lashe zaben da ke tafe.

Israel, Jerusalem: Netanjahu hält Pressekonferenz zu Atompolitik Irans
Hoto: Reuters/R. Zvulun

Tun da farko sai da duk da cewar Firaiminsta Mohammed Shtayyeh na Falasdinu ya gargade Netanyahu tare da jan hankalinsa kan ya guji yada manufofin siyasa ta hanyar amfani da yankunan kasar Falasdinawa.


Cikin shekaru gomman da Firaiminstan Netanyahu ya kwashe yana mulkin kasar wannan ne karo na farko da ya jajjirce wajen shigar da wani yanki Isra'ila.

Dubunnan Yahudawa sun yi sansani a gabar kogin Yamman tun 1967 koda yake har ya zuwa wannan lokaci Falasdinawa na ikirarin mallakinsu ne.

Al'ummar Falsadinu sun yi Allah wadai da wannan alwashi na Netanyahu tare da zarginsa da rusa shirin sulhunta yankunan biyu ta hanyar fakewa da yada manufofin siyasa.