1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Falasdinwa sun fara bin umurnin Isra'ila na gudu daga Gaza

Mouhamadou Awal Balarabe
October 13, 2023

Isra'ila ta ba da umarnin kwashe dukkan fararen hula daga zirin Gaza domin kare rayukansu daga ruwan bama-bamai da take ci gaba da kaiwa a yankin Falasdinawa, da nufin murkushe mambobin kungiyar Hamas.

Falasdinawa dauke da kayansu suna tserewa dag Gaza don gudun harin Isra'ila
Falasdinawa dauke da kayansu suna tserewa dag Gaza don gudun harin Isra'ila Hoto: Mahmud Hams/AFP/Getty Images

Wasu mazauna yankin Gaza dauke da yara suka fara taka sayyada yayin da wasu suka hau kan tireloli don gudun abin da ke je ya zo. Amma dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da matakin, yayin da ita kuma a martaninta, kungiyar Hamas t yi watsi da umurnin kaurace wa gidajensu zuwa kudanci ko kasar Masar.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya yi gargadi game da illar da ke tattare da umurnin da sojojin Isra'ila suka bayar , inda ya kwatanta shi da koran Falasdinawa 760,000 daga gidajensu a 1948, da ya gudana a shekarar da aka kasar Isra'ila. Tun dai bayan fara tashin hankalin da ya barke sakamakon wani kazamin harin da kungiyar Hamas ta kai wa Isra'ila, an kashe akalla mutane 1,300 galibi fararen hula a Isra'ila. Sai dai matakin daukar fansa da Isra'ita ta kai zirin Gaza ya yi sanadin mutuwar mutane 1,537, ciki har da yara 500.

Dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a yankin Gabas ta Tsakiya kama daga Iraki zuwa Iran da Jordan da Bahrain, domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a tashin hankalin da ake yi tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas. Wadanda suka hallara a dandalin Tahrir da ke tsakiyar Bagadaza na Iraki sun ta rera wakokin yin tir da abin da ke wakana a zirin Gaza bisa kiran shugaban 'yan Shi'a Moqtada Sadr. A Tehran da wasu birane na Iran kuwa, masu zanga-zangar sun kona tutocin Amurka da na Isra'ila, yayin da a Jordan, sama da mutane 10,000 ne suka hallara a tsakiyar birnin Amman bisa kiran kungiyar 'yan uwa Musulmi.