Fara aikin Hajjin bana da halinda ake ciki a yankin gabas ta tsakiya
December 28, 2006Akalla mahajjata miliyan uku ne aka kiyasta suke aikin hajjin na bana da aka fara yau,inda tuni alhazan suka fara kama hanyarsu ta zuwa Mina kafin wucewa tsayuwar arfa a gobe jumaa aidan Allah ya kaimu.
Hukumonmin Saudiya dai a bana sun sake sabbain tsare tsare musamman wajen jamra,domin kare sake abkuwar mace mace sakamakon turmutsutsun jamaa a wajen jamra,a bara dai mahajjata kusan 400 suka rasa rayukansu wajen yamutsin.
Yayinda miliyoyin musulmin ke fara aikin hajjin a yau don neman gafarar ubangiojinsu a wasu bangarori na duniyar musulmi kuma ana ci gaba dat tashe tashen hankula da zubda jini,misali a kasar Iraqi akalla mutane 25 ne suka halaka a yau cikin hare haren bam dake ci gaba a kasar cikin tashein hankali game da batun ratayewar tsohon shugaba Saddam Hussein.
Jamian asibiti sun sanarda cewa mutane 7 suka rasa rayukansu a cikin wata kasuwa a birnin Bagadaza,hakazalika jamian tsaro dana lafiya a asibitin abu Nafis kuma sunce wasu mutane 10 sun rasa rasukansu lokacinda bam ya fashe cikin jerin wasu mutane dake kokarin sayaen mai.
A yankin yarmuk wasu mutane 3 sun halaka hakazalika a matatatr mai ta Baiji dake kusa da garin Tikrit wasu sojojin Iraqi 2 sun rasa rayukansu.
Haka dai abin yake a wasu sassa na kasar ta Iraqi,yayinda ake zaman dakon ranar da zaa aiwatar da hukuncin kisa bisa ratayewa a kan tsohon shugaba Saddam.
Fadar gwamnatin Amurka dai tace dama tana sa ran zaa samu karin hare hare sakamakon wannan hukunci da aka yankewa Saddam,musamman daga magoya bayansa.
Kodayake daya daga cikin lauyoyin Saddam din Issam Ghazzawi ya tabbatar da sakon da Saddam din ya aike ta yanar gizo yana mai kira ga magoya bayansa da kada su nuna bacin ransu game da wannan batu,yace a shirye yake a sadaukar da kansa ga Allah.
A halinda a ake ciki dai yanzu wani jamiin jamiyar Dawwa ta shugaba Firaminista al Maliki yace gwamnati tana son a rataye Saddam ba tare da bata lokaci ba,wani jamiin kuma kusa da al Maliki yace zaa aiwatar da wannan hukunci kafin karshen kwanaki 30.
A can yankin Palasdinawa kuma Israila ta sanarda cewa,kasar Masar ta aike da dinbin makamai ga magoya bayan shugaba Mahmud Abbas.
Wani jamiin Israilan ya fadawa AFP cewa tare da hadin kan Israilan Masar ta aike da wadannan makamai ga dakarun Abbas.
Sai dai kakakin Abbas Nabil abu Rudeina ya karyata wannan zance,haka shima Muhammad Hurani wani babban jamiin Fatah ya karyata wannan batu.
Amma jamian tsaron Palasdinawa sunce tuni wadannan makamai sun isa zirin Gaza.
A cewar wata jaridar Israial Haaretz an aike da bindigogi kirar AK 47 na Kalashnikov 2,000 da harsasai miliyan 2 ga kungiyar Fatah.
Jaridar tace an kwashi wadannan makaman ne cikin manyan motoci 4 daga Masar zuwa cikin Israila ta maketarar Karem Shalom a kudancin Gaza,zuwa Karni inda jamian tsaro na hukumar Palasdinawa suka amsa.
Aikewa da makaman ya biyo bayan tattaunawa ce tsakanin Israila da Masar da Amurka kuma an kammala yanke shawawar ce a taron ranar asabar tsakanin Ehud Olmert da Abbas a birnin Qudus.
Kasar Israila wadda tare da kasashen yammam suka dauki kungiyar Hamas a matsayin kungiyar taadda,suna kokarin karfafa kungiyar Mahmud Abbas a fito na fito da sukeyi da magoya bayan Hamas.