1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ibadar Azumin Ramadan a fadin duniya

Yusuf BalaJune 17, 2015

Mahukunta a Saudiyya da Iran da Indonesiya da sauran wasu kasashen na Musulmi sun bayyana cewa da zarar an ga jinjirin watan Ramadhana a fara azumi Alhamis.

Indonesien Lesende Muslima
Musulmi na karatun Qur'aniHoto: picture-alliance/ys1/ZUMA Press


Musulmi a fadin duniya na daf da fara ibadar watan Azumin Ramadan, ibadar da akan fara tun daga billowar alfijir zuwa faduwar rana tsawon wata guda.

Mahukunta a kasashen Saudiyya da Iran da Indonesiya da sauran wasu kasashen na Musulmi sun bayyana cewa da zarar an ga jinjirin watan Ramadan a yammacin na Laraban nan za a tashi da azumi a ranar Alhamis.

Wannan wata dai mai tsarki na Ramadan a shi ne al'ummar Musulmin duniya ke kara azama wajen ibada dan neman kusanci da mahalicci Allah. A kowace rana cikin watan da zarar rana ta fadi Musulmi kan bude baki da ruwa ko dabinu ko dai abin da ya sauwaka.