Fara kai hari kan 'yan fashin tekun Somaliya
May 18, 2012A labarin da ta buga game da farmakin jaridar Süddeutsche Zeittung cewa ta yi:
"Tawagar rundunar sojin ruwa ta Atalanta ta lalata sansanonin 'yan fashin teku a doron ƙasa, lamarin da ko tantama babu ke da muhimmanci a fannin aikin soji, domin ƙara matsa ƙaimi akan 'yan fashin jirgin ruwan Somaliya. Yayin da a lokutan baya sojojin na EU suka taƙaita aikinsu akan fatattakar 'yan fashin a cikin teku, yanzu sun faɗaɗa aikinsu inda a karon farko suka yi amfani da jiragen saman yaƙi masu saukar ungulu akan sansanonin 'yan fashin a cikin ƙasar ta Somaliya."
A labarin da ta buga game da farmakin jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung yabawa ta yi da harin ne kasancewa in ban da sansanonin 'yan fashin teku da aka lalatata babu wani ɗan Somaliya da aka yiwa rauni. An tabbatar da tsaron lafiyar 'yan Somaliya mazauna gabacin ƙasar, da masunya da su ma kansu ta'asar 'yan fashin tekun ta addabe su. Kuma ƙungiyar tarayyar Turai ta tabbatar cewa a nan gaba ma za ta ci-gaba da kare lafiyar fararen hula da ba ruwansu da aika-aikar 'yan fashin tekun na Somaliya."
An fusata da 'yan tawayen FDLR da sojojin duniya
Ita kuwa jaridar die Tageszeitung labari ta buga game da halin da ake ciki a gabacin Kongo tana mai cewa haƙurin 'yan ƙasar ta Kongo ya ƙare game da ƙungiyar 'yan tawayen Hutu ta FDLR da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya.
"Al'ummar yankin Kivu dake gabacin Jamhuriyar Demokraɗiyya Kongo sun gaji da ta'asar sojojin sa kai na ƙungiyar 'yan tawayen Hutun Rwanda. Bayan jerin kisan kiyashi a yankin a ranar Litinin da ta gabata mazauna yankin sun huce hushinsu a kan sojojin Majalisar Ɗinkin Duniya a garin Bunyakiri dake kudancin Kivu bisa zarginsu da rashin ɗaukar wani mataki a kan 'yan tawayen na ƙungiyar FDLR. Sojoji 11 daga ƙasar Pakistan aka yi wa rauni huɗu rauni mai tsanani. Hakan ta zo ne bayan wani hari da 'yan tawayen FDLR suka kai kan wani ƙauye da sanyin safiyar ranar Litinin, inda suka halaka fararen hula shida. A ranar huɗu ga watannan na Mayu ma mayaƙan FDLR ɗin sun kai wani hari a wani ƙauye dake yankin na Kivu inda suka kashe mutane 11. Tun farkon wannan wata na Mayu mutane 30 suka rasa rayukansu a yankin sakamakon ta'asar ta 'yan tawayen FDLR."
Gwamnatin Madagaska na cikin wadi na tsaka mai wuya
Ita kuwa jaridar Neues Deutschland ta mayar da hankali ne a kan gazawar gwamnatin Madagaska wajen magance rikicin ƙasar, tana mai cewa hauhawar farashin kaya da yawan aikata laifuka na ƙara jefa gwamnatin wucin gadi cikin halin tsaka mai wuya. Gwamnatin riƙon ƙwarya ƙarƙashin shugaba Andry Rajoelina da ya fara jan ragamar ƙasar bayan wani juyin mulki a shekarar 2009, tana ƙara fuskantar matsalolin taɓarɓarewar halin rayuwar 'yan ƙasa, inda a kullum ake gudanar da zanga-zangar ƙin jininta. Abin damuwa ma shi ne ta kasa gano hanyoyin magance waɗannan matsalolin.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman