Lafiya
Amirka: Riga-kafi ga daga shekara biyar
November 3, 2021![USA | Pfizer-BioNTech Covid-19 Impfung für Kinder in Hartford](https://static.dw.com/image/59703582_800.webp)
Talla
Wannan matakin dai na zuwa ne, biyo bayan shawarar da Hukumar Kula da Cutuka Masu Yaduwa ta Amirkan CDC ta bayar, na bukatar a yi wa yaran allurar riga-kafin samfurin Biontech/Pfizer. Tuni dai aka fara yi wa wasu yaran wannan riga-kafin, bayan da Hukumar Tantance Ingancin Abinci da Magunguna ta kasar ta amince da shawarar hukumar ta CDC a karshen makon da ya gabata. Kawo yanzu dai, mahukuntan Amirkan sun fara rarraba karin alluran a sassan kasar dabam-dabam.