1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da dokar 'yan fansho a Faransa

Abdoulaye Mamane Amadou
December 17, 2019

Gangamin adawa da sabon tsarin siyasar ritaya da na 'yan fansho a Faransa ya dauki wani sabon salo inda kungiyoyin kwadago suka sake kiran yajin aikin gama-gari da wata gagarumar zanga-zanga.

Frankreich Streik | Metro in Paris
Hoto: Getty Images/AFP/M. Bureau

Yajin aikin na ci gaba da daidaita fannoni da dama na kasar musamman ma fannin sufurin jama'a da na kasuwanci a daidai lokacin da bukukuwan Kirismeti ke kara karatowa.

Tuni firaministan kasar ya gayyaci kungiyoyin 'yan kwadagon kasar zuwa wata tattaunawa a ranar Laraba, a yunkurin da hukumomin kasar suke ta yi na neman kawo masalaha tsakanin bangarori da dama da ke adawa da sabuwar dokar.