1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaFaransa

Faransa: Adawa da tsuke bakin aljihun gwamnati

Abdullahi Tanko Bala
September 18, 2025

Masu zanga zanga a Faransa sun kawo tsaiko ga ababen hawa tare da toshe hanyoyi a fadin Faransa a yau Alhamis a wani mataki na nuna adawa da shirin shugaba Emmanuel Macron na tsuke bakin aljihun gwamnati

Zanga zangar kungiyoyin kwadago a birnin Marseille na Faransa
Hoto: Clement Mahoudeau/AFP/Getty Images

Masu zanga zangar sun toshe hanyoyin jiragen kasa a birnin Paris da hanyoyin mota da suka hade da wasu gundumomi yayin da zanga zangar ke ci gaba da yaduwa daga manyan birane zuwa kananan garuruwa.

A birnin Paris da Marseille 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa gangamin da hukuma ta haramta.

Kungiyoyin kwadago da dama sun shiga zanga zangar domin kiran gwamnati ta yi watsi da shirin rage kasafin kudi a kan harkokin walwala da jin dadin al'umma da sauran bangarori da suka ce zai kuntata wa masu karamin karfi da matsakaitan ma'aikata.

Sun ce shirin tsuke bakin aljihun zai kara matsin tattalin arziki, matakin da a baya ya jawo rushewar gwamnatotoci a kasar a yanzu kuma yake neman maimaita kansa da makamancin shirin garanbawul da gwamnatin ke son aiwatarwa.