1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Faransa: Attal ya kasance firaminista mafi karancin shekaru

January 9, 2024

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya nada Gabriel Attal, a matsayin sabon firaministan kasar, da zai cike gibin da aka samu bayan murabus din Elisabeth Borne, wacce shugaban ya amince da murabus din ta.

Hoto: Raphael Lafargue/abaca/picture alliance

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya nada Gabriel Attal, a matsayin sabon firaministan kasar, da zai cike gibin da aka samu bayan murabus din Elisabeth Borne, wacce shugaban ya amince da murabus din ta.

Gabriel Attal, dan shekara 34, ya kasance mafi karancin shekaru kuma dan neman jinsi dayn wanda zai jagoranci daya daga cikin kujeru mafi girma a tsarin mulkin kasar ta Faransa.

Babban aikin da ke gaban sabon firaministan shi ne kafa sabuwar gwamnati ta hanyar gudanar da garambawul mafi girma a majalisar zartaswar kasar, a shekaru ukun da suka ragewa mulkin Emmanuel Macron.

Wannan garambawul na zuwa gabanin gasar Olympic da za a gudanar a birnin Paris a bana, da kuma zaben 'yan majalisa Kungiyar Tarayyar Turai da za a gudanar a lokacin bazara.

Sai dai kididdigar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewar jam'iyyar Macron ka iya fuskantar kalubale daga hannun babbar 'yar adawarsa mai kyamar baki Marine Le Pen.