1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa: Bardella ya zama shugaban jam'iyyar Le Pen

November 6, 2022

Babbar jam'iyyar adawar Faransa mai ra'ayin rikau ta RN ta zabi matashi Jordan Bardella dan shekaru 27 domin ya maye gurbin Marine Le Pen wacce ta gaza kayar da Shugaba Emmanuel Macron.

Frankreich I Jordan Bardella I Regional- und Abteilungswahlen  des Rassemblement National
Jordan Bardella, sabon shugaban jam'iyyar Marine Le Pen ta FaransaHoto: Berzane Nasser/ABACA/picture alliance

Bardella ya samu wannan nasara ce bayan fafatawar da ya yi da Louis Aliot a wannan Asabar, inda ya samu kaso 85 cikin 100 na kuru'un 'yan jam'iyyar.

Ana sa ran ya ci gaba da aikin gina mutuncin jam'iyyar a fadin Faransa bayan shekaru 11 da Marine Le Pen ta yi tana wannan aiki.

Duk da gaza kayar da shugaba Emmanuel Macron da Le Pen ta yi a zaben shugaban kasar da ya gabata a shekarar nan, rahotonni sun ce 'yar siyasar yanzu za ta mayar da hankalinta ga samun goyon bayan 'yan majalisar kasar domin sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.