1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa da Beljiyam za su amince da kafa kasar Falasdinu

September 22, 2025

Tun da fari, kasashen Birtaniya da Canada da kuma Australiya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York a Amurka
Zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York a AmurkaHoto: Lev Radin/Pacific Press/picture alliance

Ana sa ran kasashe da dama a wannan Litinin din su amince da kafa kasar Falasdinu, gabanin fara babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya da zai gudana a birnin New York na kasar Amurka. Kasashen Faransa da Saudiyya ne za su jagoranci taron da zai mayar da hankali a kan samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu na Isra'ila da kuma Falasdinu.

Kasashen Faransa da Beljiyam da New Zealand duk sun ce za su amince da Falasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta duk da cewa Isra'ila na adawa da hakan. A ranar Lahadi Birtaniya da Canada da Asutraliya suka amince da Falasdinu a matsayin kasa.

Karin bayani: Burtaniya ta amince da Falasdinu a matsayin kasa

Isra'ila da Amurka sun ce za su kaurace wa taron yayin da Ministan harkokin wajen Jamus, Johann Wadephul zai halarci taron nuna goyon baya, sai dai fadar gwamnatin Berlin ba ta shirya amince wa da kafa Falasdinu ba.