1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta nisanta kanta da zama kanwa uwar gami

Abdoulaye Mamane Amadou ATB
August 28, 2023

Shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa ya nisanta kasar da zama ummul-haba-isin abubuwan da ke faruwa a kasashen nahiyar Afirka ciki har da yankin Sahel.

Emmanuel Macro I Mohamed Bazoum I Paris I 16/02/2023
Shugaba Macro yana karbar bakwancin Mohamed Bazoum a birnin Paris ranar 16/02/2023 Hoto: Michel Euler/AP/picture alliance

Shugaba Macron ya furta kalamun ne a yayin da yake ganawa da jakadun kasashen Afirka a birnin Paris, inda ya kara da cewa da akwai kasawar Faransa da ba ta kasance a ko ina ba, kana a cikin jawabinsa Macron ya ce ya kwan da sanin jami'an diflomasiyar Fransa a ko ina cikin duniya sun fuskanci tarnaki.

Karin Bayani: Sabuwar baraka tsakanin Nijar da Faransa

Shugaba Emmanuel Macron ya ce "Faransa da jami'an diflomaisyyarta sun kasance a cikin mawuyacin hali a wasu kasashen nahiyar Afirka a 'yan watannin nan, misali a Sudan da Faransa ta zama misali, bayan kwashe 'yan kasarta da wasu 'yan kasashen ketare, ko a Nijar inda yanzu hakan jakadanmu ke ci gaba da aiki da kuma ke saurarenmu a yanzu."

Karin Bayani: Kadawar guguwar sauyi a yammacin Afirka

Kalamun shugaban na zuwa daidai lokacin da guguwar juye-juyen mulki ke daukar dumi a yankin Sahel ciki har da Nijar, kasar da sojojin da suka kifar da gwamnati suka umarci jakadan Faransa da ya fice daga kasar a cikin tsukin sa'o'i 48, matakin da fadar gwamnatin Elysee ta yi fatali da shi.