1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Inganta alakar Aljeriya da Faransa

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 25, 2022

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya fara wata ziyara ta kwanaki uku a Aljeriya, a wani kokari na farfado da dangantakar da ta yi tsami a tsakaninta da kasar da ta yi wa mulkin mallaka.

Faransa | Emmanuel Macron | Aljeriya | Ziyara
Ko Shugaba Emmanuel Macron na Faransa zai iya gyara alakar kasarsa da Aljeriya?Hoto: Christophe Ena/AP Photo/picture alliance

Ziyarar ta Shugaba Emmanuel Macron da ke zaman shugaban Faransa da aka haifa bayan Aljeriya ta samu 'yancin kanta, na zuwa ne a daidai lokacin da Agiers din ke bikin cika shekaru 60 da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na Faransan. Macron din dai na fatan ziyarar tasa za ta kawo karshen zaman 'yan marina da suke yi, tare da kasar da Faransan ta raina da ke yankin arewacin Afirka. Yayin ziyarar tasa Macron da mai masaukinsa Shugaba Abdelmadjid Tebboune na Aljeriya, za su ziyarci wuraren tarihi da kaburburan mutane da suka halaka a yakin neman 'yancin kai na Aljeriyan da aka kammala sama da shekaru 130 da suka gabata.