1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaFaransa

Sarkozy zai gurfana gaban kuliya a 2025

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 25, 2023

Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy zai fuskanci tuhuma, dangane da zargin karbar makudan kudi a hannun tsohon shugaban mulkin kama-kayaryar kasar Libiya marigayi Muammar Gaddafi domin yakin neman zabensa.

Faransa | Nicolas Sarkozy | Tsohon Shugaban Kasa
Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas SarkozyHoto: Bertrand Guay/AFP/dpa/picture alliance

A shekara ta 2025 ne dai ake sa ran za a fara sauraron shari'ar da kuma shaidu, inda ake zargin Nicolas Sarkozy da ke zaman dan jam'iyyar masu tsan-tsan ra'ayin kishin kasa da wasu mutane 12 da hada kai suka karbar makudan kudi a hannun tsohon shugaban kasar Libiyan marigayi Muammar Gaddafi ba bisa ka'ida ba, domin daukar nauyin takararsa ta shugaban kasa a zaben shekara ta 2007.