Faransa: Karon batar karfe tsakanin Macron da Le pen
May 7, 2017Tuni dai Emmanuel Macron ya kada kuri'ar sa a garin Le Touquet a yayin da Marine Le Pen ta kasance a karamar hukumar Henin-Beaumont in ta kada kuri'a. Ofishin ministan cikin gida na kasar ya bayyana cewaR ya zuwa tsakiyar ranar ta yau adadin mutanen da suka fito zaben ya kai kaso 28,23% na wadanda suka cancanci kada kuri'ar ta su. Hasashen jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan sun bayyana Emmanuel Macron a matsayin wanda zai lashe zaben da kaso 61,5%.
Sai dai nasarar ba zata da Donald trump ya samu a zaben Amirka da ma yadda masu goyon bayan ficewar Birtaniya daga Kungiyar EU wato Brexit suka samu ta sanya Faransawar da dama yin taka tsantsan a game da hasashen jin ra'ayin jama'a musamman a game da fargabar da ake da ta yiwuwar samun mutane da dama da za su yi rowar kuri'un su.