Faransa ma za ta kai hari ta sama a Iraki
September 18, 2014Talla
Faransa ta ce za ta marawa Amirka baya wajen kai hare-hare ta sama kan mayakan IS wadanda ke da'awar kafa kasa ta Islama bayan da suka wallafa wasu hotunan bidiyo na wani dan asalin kasahen yamman da suka yi garkuwa da shi. Sai dai ba kaman sauran hotunan yan jaridan Amirka nan biyu da na ma'aikacin agajin Birtaniyan nan da suka turo ba, inda suka gwado yadda aka fille musu kawunansu.
A wannan karon sun nuno dan jaridar Birtaniyar John Cantlie ya na magana ne yana kallon abin daukar hoton kamar dai yadda ya ke karanta labarai. Wannan mataki na Faransa na zuwa ne a daidai lokacin da Washington ke neman amincewa da shirin koyar da 'yan tawayen Siriya domin su yaki kungiyar mayakan IS ganin yadda ta kara karfi a yan kwanakin baya-bayan nan.