Faransa: Maikatan jirgin kasa na yajin aikin gama gari
April 3, 2018Talla
Ma'aikatan jirgin kasa a Faransa a yau Talata sun fara yajin aikin sai baba ta gani na watanni uku, a wani matakin yan kwadagon dake zama zakaran gwajin dafi ga shugaban kasar Emmanuel Macron a yunkurinsa na yin garanbawul ga harkokin kwadago.
Zanga zangar dai za ta haifar da rudani a sufurin jiragen kasa ga jama'a kimanin miliyan biyar a Faransar wadanda ke amfani da jirgin kasa a harkokin su na yau da kullum.
Ma'aikatan za su rika yajin aiki ne kwanaki biyu a kowane mako har zuwa ranar 28 ga watan Juni matukar shugaba Macron bai jingine aniyarsa ta garanbawul ga harkar sufurin jiragen kasar ba.
Ma'aikatan kamfanin jirgin sama na Air France da masu kwashe shara da ma'aikatan makamashi su ma suna shirin shiga yajin aiki a ranar Talata.