Faransa na ɗaukar ƙarin matakai na yaƙi da ta'addanci
November 22, 2014![Frankreich Premierminister Manuel Valls](https://static.dw.com/image/17551695_800.webp)
Talla
Firaministan ya ƙara jaddada aniyar ƙasarsa ta ƙara ƙaimi wajan ɗaukan matakai kan sabon salon ta'addanci da 'yan jihadi ke yi. Manuel Valls ya yi wannan furci ne a wannan Asabar ɗin a birnin Ndjamena na ƙasar Chadi, inda ya ziyarci rundunar sojan ƙasar ta Faransa wacce ake kira da sunan Barkhane da ke da aƙalla sojoji 1.300 a wannan ƙasa.
Da yake jawabi a gaban sojojin Firaministan ƙasar ta Faransa ya ce, ya na mai biye da su sau da kafa kan iri-irin aiyyukan da suka yi a 'yan makonnin baya-bayan nan, wanda hakkan ya sanya masu tadda ƙayar bayan suka gaza samun sukuni tare da rage musu karfi sossai.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hassane