SiyasaGabas ta Tsakiya
Faransa na son a kakaba takunkumai kan shugabannin Hamas
November 23, 2023Talla
Faransar na son Tarayyar ta Turai ta dora takunkuman a kan daidaikun jagoroin kungiyar Hamas ne, ganin a yanzu kungiyar ta EU ta tsaya ne kawai a kan matsayin Allah wadai a kan abin da kungiyar ta aikata.
A cewar sakatariyar harkokin ketaren faransa musamman kan al'amuran Tarayyar Turai, Laurence Boone, takunkuman za su shafi kudi ne kai tsaye musamman ma rufe asusunsu na bankuna.
Matakin kamar yadda Faransa da EU ke son yi, zai kuma shafi har da kawayen Hamas da kuma kungiyar Hizbollah, makamancin wanda aka dora wa jami'an kasar Iran da ke taimaka wa yakin da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine.