1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta ƙaddamar da yaƙi kan Libiya

March 19, 2011

Jim kaɗan bayan taron shugabanin manyan ƙasashen duniya a Paris, jiragen yaƙin Faransa sun fara kai farmaki a Libiya

Khaddafi ya shiga halin damuwaHoto: AP / United Nations

A wannan Asabar ne a birnin Paris an ƙasar Faransa aka kamalla wani mahimmin zaman taro, wanda ya haɗa sakaratiyar harakokin wajen Amurika Hilary Clinton, shugaba Faransa Nikolas Sarkozy shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel,da takwaranta na Birtaniya David Camaeron, da kuma Sakatare Janar na Majalisa Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon, da dai sauran wakilai daga ƙasashen Turai da na larabawa.

Mahalarta taron, sun bayana ɗaukar matakan soja da zumar ceton al´umomin ƙasar Libiya da a yanzu haka ke cikin uƙuba, dalili da yaƙin da ake gwabzawa tsakanin dakarun shugaba Mohamar Ƙaddafi da ´yan tawaye.

A yayin da ya ke bayani jim kaɗan bayan taron, shugaban ƙasar Faransa Nikolas Sarkozy ya ce ƙasarsa a shirye ta ke, yanzunan ma,ta fara kai hari a Libiya.

Sarkozy ya ci gaba da bayani ya na cewa:Ina faɗi da babbar murya cewa, a yanzu fa lokaci yayi na kowa ya ɗauki yaunin da ya rataya kansa.Matakin da mu ka ɗauka yau, na da matuƙar mahimmanci.Tare da sauran ƙasashen duniya, Faransa za ta taka rawar da ta dace a cikin wannan marra.

A daidai kimanin ƙarfe biyar agogon GMT, jiragen yaƙin Faransa su ka fara luggudan wuta a ƙasar Libiya.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal