1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Me ya sa Faransa ke son kama Bashar al-Assad?

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim AH
January 22, 2025

Hukumar kula da harkokin shari'a ta kasar Faransa ta ba da izinin kamo hambararren Shugaban Syria Bashar al-Assad, bisa zargin aikata laifukan yaki tare da halaka wani dan Faransa mai tushe da Siriya a shekarar 2017.

Tsohon shugaban kasar Syria, Bashar al-AssadHoto: SANA/Photoshot/picture alliance

Binciken jami'an hukumar ya zargi Assad da halaka fararen hula ba gaira ba dalili ta hanyar kai musu hare-hare da makamai masu guba, wanda dakarun sojin kasar suka kai garin Ghouta da ke kusa da birnin Damascus a shekarar 2013 da ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwar jama'a, ko da yake rahoton kungiyoyin kare hakkin bil'adama ya nuna cewa mutanen da suka mutu sun haura dubu daya.

An kai irin wannan hari na guba a birnin Daraa a shekarar 2017. Tun a cikin shekarar 2023 ne Faransa ta fara ba da sammacin kamo Bashar al-Assad, wanda mayakan 'yan tawayen HTS suka kawar daga kan karagar mulki a cikin watan Disamban shekarar 2024 da ta gabata, inda ya arce zuwa birnin Moscow na Rasha don samun mafakar siyasa.