Faransa ta bukaci kare rayukan fararen hula a Siriya
November 30, 2024Kazalika shugaban ya kuma bukace su da su kula da rayukan fararen hula da a koda yaushe ke zama a tsakiyar rikici idan ya ta so.
Kiran na Macron na zuwa ne bayan da mayaka masu jayayya da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad na Syria, suka kwace iko da kusan dukkanin yankunan Aleppo, wanda ke birni na biyu mafi girma a kasar.
Kungiyar da ke sa ido don kare hakkin al'umma a Syria wato Syrian Observatory for Human Rights, ta ce gamayyar kungiyoyin tawaye karkashin jagorancin kungiyar Hayat Tahrir al-Sham sun danna zuwa birnin na Aleppo inda suka kwace galibin yankin na arewacin kasar.
A halin yanzu dai gwamnan birnin da kwamandodjin tsaro duk sun janye daga tsakiyar Aleppon, yayin kuma da dakarun gwamnati ke arcewa zuwa kauyuka da ke kewayen yankin.
Sai dai sojojin Syriarna cewa yawan mayakan na tawaye, ya sanya su sake salo na yaki, inda a yanzu suka ja daaga domin yin amfani da wasu dabaru na maida martani.