Faransa ta ce sansanta Rasha da Ukraine zai dauki watanni
February 8, 2022Bayan tattaunawar da ya yi da shugabannin kasashen Rasha da Ukraine, Shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa, ya ce ya ga alamun iya kawo karshen sabuwar kiki-kakar nan da ta kunno kai a tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Macron dai ya gana da takwaransa, Volodimyr Zelensky na Ukraine a wannan Talata, kwana guda bayan kwashe sa'o'i biyar yana tattauanwa da Shugaba Putin na Rasha a jiya Litinin a kan batun.
Mr. Macron ya ce ba za su raina wannan rikici da kunno kai a tsakanin kasashen biyu ba, sannan wani hanzari kuma rikicin abu ne da ake kwashe watanni kafin a iya warware shi.
Shugaban na Faransa zai kuma tattauna da shugabannin gwamnatocin Jamus da na Poland a birnin Berlin da yammacin wannan Talata.
Duk dai a kokarin fifita diflomasiyya a rikicin da zargi ya yi karfi a kan Rasha na nuna kokari ne na mamaye gabashin Ukraine.