1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta dakatar da taimakon raya kasa ga Nijar.

Abdullahi Tanko Bala
July 29, 2023

Sakamakon juyin mulki a Nijar Faransa ta sanar da dakatar da bai wa kasar taimakon raya kasa har sai an mayar da ita kan mulkin dimukuradiyya.

Screenshot DW Sendung Niger
Hoto: DW

Faransar har ila yau ta yi kiran gaggauta mayar da kasar kan tafarkin tsarin mulki tare da mayar da Bazoum wanda aka zaba ta hanyar dimukuradiyya kan mukaminsa.

A shekarar 2021 hukumar raya kasashe ta Faransa ta baiwa Nijar daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya tallafin kudi euro miliyan 97 kamar yadda alkaluman da hukumar ta wallafa a shafinta na yanar gizo ya nunar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin ziyarar da ya kai Papua New Guinea a ranar Juma'a ya yi Allah wadai da juyin mulkin sojin wanda ya baiyana da cewa abu ne mai matukar hadari ga yankin. Ya kuma bukaci a sako Bazoum wanda sojojin ke tsare da shi a gidansa tun a ranar Laraba.

Kasar Nijar dai na daya daga cikin kasashe aminan Faransa a yankin Sahel, yankin da ke fama da matsalalolin rashin tsaro da hare haren mayakan jihadi.

Juyin mulkin na Nijar shi ne na uku tun shekarar 2020 bayan karbe mulki da sojoji suka yi a kasashen Mali da Burkina Faso.