1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Faransa ta fara janye jami'an diflomasiyyarta daga Mali

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 21, 2025

Faransa ta ce yawaitar hare-haren ta'addanci sun janyo zaman dai-dar cikin tsoro da fargaba a kasar ta yammacin Afirka.

Yadda sojojin Faransa ke barin sansaninsu na yanmin Gossi a kasar Mali cikin shekarar 2022
Hoto: Etat-Major des Armees/ABACAPRESS.COM/picture alliance

Faransa na shirin rage jami'an diflomasiyyarta na kasar Mali, sanadiyyar tabarbarewar tsaro da ke kara munana a kasar daga kungiyoyi masu ikirarin jihadi.

Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta ce yawaitar hare-haren ta'addanci sun janyo zaman dar-dar cikin tsoro da fargaba, a kasar ta yammacin Afirka, ko da yake za ta ci gaba bibiyar halin da ake ciki.

Karin bayani:Nijar: Matasan da ke zuwa Mali na komawa gida

Tuni dai kasashen irin su Amurka da Burtaniya suka fara kwashe wasu jami'an diflomasiyyarsu daga kasar, domin kare rayukansu daga hare-haren ta'addanci, wanda ke ci gaba da haddasa asarar rayukan jama'a ba adadi.