1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaHaiti

Faransa ta fara kwashe 'yan kasarta daga Haiti

Abdoulaye Mamane Amadou
March 27, 2024

Sakamakon kazancewar rikici da farmakin da 'yan daba ke kai ba kakkautawa, gwamnatin Faransa ta fara kwashe 'yan kasarta da ke zama a kasar Haiti.

Hoto: Hansenn/Zoonar/picture alliance

Faransawa fiye da 170 da wasu al'ummar nahiyar Turai 70 ne sun fice daga birnin Port-au-Prince na kasar Haiti, a karkashin wani shirin da gwamnatin Faransa ta kaddamar na kwashe 'yan kasarta daga kasar wacce 'yan daba suka mamaye.

Karin Bayani: Faransa za ta fara kwashe jama'arta daga Haiti

Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta ce an yi nasarar kwashe mutanen ne daga wani jirgi mai saukar ungulu da ya tashi daga Haiti zuwa gabar ruwa ta Fort-de-France.

Daman dai tun a karshen makon jiya, hukumomin na Faransa suka bayyana anniyarsu ta kwashe daukacin al'ummar kasar da ke da bukatar ficewa daga Haiti, kasar da sannu a hankali rikice-rikice ya yi mata katutu.

Karin Bayani: Firaministan Haiti ya yi murabus daga mukaminsa

Faransa na da 'yan kasarta dubu da 100 da ke rayuwa a Haiti a cewar wasu alkaluman da fadar Quai d'Orsay ta bayyana.