1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Faransa ta haramta shan taba sigari a wasu wurare

Binta Aliyu Zurmi
June 29, 2025

Dokar hana shan taba sigari a bainar jama'a mussaman inda yara kananan suke, a kasar Faransa ta fara aiki.

Bangladesch | Tabakkonsum
Hoto: DW

Wuraraen da aka haramta shan sigarin sun hada da tashoshin mota da bakin teku da kusa da matarantu da ma duk wani waje da yara kanana suke kai komo.

Mahukuntan na Faransa sun baiyyana wannan mataki da kokari na kare al'ummar da basa shan taba sigari shakar hayakin dake da illa.

Ministar lafiya ta Faransa Catherine Vautrin ta ce duk wanda aka kama da karya dokar za a ci shi tarar euro 135 kwatankwacin naira a  kusan dubu 250,000.

Zukar taba sigari na daga cikin manyan kalubalen lafiya da al'ummar Faransa ke fama da shi, a cewar ministar a duk shekarar sama da mutane 75,000 ne ke mutuwa sanadin illar hayakin sigari.