1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta janye dakarun Barkhane daga Mali

November 11, 2022

A hukumance, Shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa ya sanar da kawo karshen aikin rundunar nan ta Barkhane da ke yaki da ta'addanci a kasar Mali.

Operation Barkhane in Mali
Hoto: Philippe De Poulpiquet/MAXPPP/dpa/picture alliance

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, ya sanar da yanjewar dakarun Barkhane din ne bayan da dakarun ficewa ta karshe da rundunar ta Barkhane suka yi daga Malin cikin watan Agusta.

Sai dai bayan shekaru tara da mayakan na Barkhane suka kwashe suna sintiri a kasar da ke yammacin Afirka, Shugaba Macron ya ce Faransa za ta ci gaba shiga al'amuran tsaro a yankin Sahel, amma ta wata sigar.

Sabuwar sigar a cewar shugaban na Fransa, ita ce ta aiki da sojojin za su a fakaice ba kuma a matsayin runduna ta sosai ba, sai dai bai bayar da wa'adin wannan sabon tsari ba.

Har yanzu dai akwai sojojin Faransa dubu uku da ke baje a kasashen Nijar da Chadi da ma Burkina Faso suna yaki da ayukkan mayakan tarzoma da sunan jihadi.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW

Karin labarai daga DW