Faransa ta karrama gawar Arnaud Beltrame
March 28, 2018A kasar Faransa an gudanar a wannan laraba da taron karrama gawar Kanal Arnaud Beltrame jami'in tsaron da ya sadaukar da ransa wajen ceto wata mata da wani dan ta'adda ya yi garkuwa da ita a lokacin wani harin ta'addanci da ya kai a ranar Juma'ar da ta gabata a garuruwan Carcassonne da Trebes inda mutane hudu suka hallaka.
Daruruwan Faransawa ne dai da suka hada da iyali, dangi, 'yan uwa da aminnan arziki na marigayin suka hallara a wajen taron karramagawar mamacin da ya gudana a birnin Paris a safiyar wannan Laraba. Da yake jawabi a wajen wannan taro, Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana Kanal Aranaud Bertrame a matsayin jarumi.
A gobe Alhamis ne dai za a gudanar da jana'izar marigayin a garin Ferrals a kudancin Faransa. A ranar Juma'ar da ta gabata ce dai wani matashi mai suna Radouane Lakdim ya hallaka jami'in tsaro wanda ya amince ya mika kansa gareshi a madadin wata mata da ya yi garkuwa da ita.