1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Faransa ta musguna wa Kamaru - Macron

August 13, 2025

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kasarsa ta musguna wa mutane lokacin mulkin mallaka a Kamaru.

Amincewar ta biyo bayan wani rahoto ne da aka wallafa a hukumance a watan Janairu, wanda ya ce Faransa ta tilasta wa jama'a da yawa yin hijira.
Amincewar ta biyo bayan wani rahoto ne da aka wallafa a hukumance a watan Janairu, wanda ya ce Faransa ta tilasta wa jama'a da yawa yin hijira.Hoto: Stephane Lemouton/abaca/picture alliance

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya amince cewa kasarsa ta musguna wa al'ummar Kamaru a lokacin da ta yi mata mulkin mallaka har zuwa samun 'yancin kai a tsakanin shekarun 1950.

Macron ya fadi haka ne a wata wasikar da ya fitar wacce ta kunshi irin jerin abubuwa da Faransa ta aikata a Kamaru kuma aka wallafa wasikar a ranar Talata.

Tsofaffi sun mamye siyasar Afirka

 Wasikar, wacce aka tura wa takwaransa na Kamaru a watan da ya gabata, na daga cikin sabbin misalan yadda Faransa a karkashin Macron ke kokarin fito da abubuwa da suka faru yayin mulkin mallakar da ta yi.

Amincewar ta biyo bayan wani rahoto ne da aka wallafa a hukumance a watan Janairu, wanda ya ce Faransa ta tilasta wa jama'a da yawa yin hijira.

Kamto ya yi tir da watsi da takararsa a zaben shugaban kasa

Wasikar ta kuma amince cewa Faransa ta tura dubban 'yan Kamaru sansanonin gwale-gwale tare da goyon bayan kungiyoyin ‘yan bindiga domin murkushe yunkurin neman ‘yancin kai na kasar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW