Faransa ta bukaci China ta yi da gaske kan sauyin yanayi
November 2, 2015Shugaban kasar Faransa Francois Hollande a ranar Litinin din nan ya bayyana cewa tallafin da kasar China za ta bayar kan batun cimma matsaya a taron koli da za a yi nan gaba a birnin Paris, abu ne da ke zama mai muhimmancin gaske. Shugaba Holland ya bayyana haka ne a ziyarar da ya fara a wannan kasa da ke zama babba a nahiyar Asiya.
Da yake jawabi a birni na Chongqing da ke a kudu maso yammacin China ya ce yana cike da fata na ganin shugabannin kasashen duniya sun ba da hadin kai da ya dace ta yadda za a rage dimamar yanayi ya zuwa digiri biyu a ma'aunin zafi. Ya ce tallafin na China gagarumi ne kasancewar batun na sauyin yanayi abu ne da ya shafi baki dayan al'ummar duniya, ta yadda za a yi tattalin muhallin dan Adam, kuma batu ne da ke da muhimmanci ga tattalin arzikin kasashen a fafutikar da ake ta ganin an samar da ci-gaba ba tare da gurbata muhalli ba ta hanyar abin da ake kira green growth a Turance.
China dai na zama kasa da tafi gurbata muhalli a duniya wacce ake ganin tana da abin cewa a taron kolin kan sauyin yanayi da za a fara daga ranar 30 ga watan nan na Nuwamba.