Faransa ta sanar da lokacin janye dakarunta daga Mali.
July 9, 2021Talla
Shugaba Emmanuel Macron na faransa ne ya bayyana hakan a wajen taron da suka gudanar tare da shugabanin kasashen kungiyar G5 Sahel a birnin Paris, sai dai Macron din ya ce kasar tasa za ta cigaba da kawance da kasashen na kungiyar ta tsaro, da suka hada da Mali da chadi da Murtaniya da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar wajen yaki da 'yan ta'adda a yankin.
A wajen taron shugaba Bazoum Muhammed na jamhuriyar Nijar ya ce sun cimma wata 'yar kwarya-kwaryar yarjejeniya da makwabciyar kasar tasa ta tarayyar Najeriya wajen mayar da 'yan gudun hijira sama da 1,300 matsugunnansu da hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram ya rabasu da gidajensu.