1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Faransa ta tsananta tsaro bayan hari a Rasha

March 25, 2024

Bayan harin ta'addanci da aka kaddamar a kasar Rasha a karshen makon jiya, Faransa ta tsaurara matakan tsaro zuwa babban mataki. Hari ne dai da kungiyar IS ta dauki alhaki.

Jami'an 'yan sanda a birnin Paris na kasar Faransa
Jami'an 'yan sanda a birnin Paris na kasar FaransaHoto: Stephanie Lecocq/REUTERS

Faransa ta kara matakan ankararwarta zuwa mataki na kololuwa, bayan mumunan harin nan da aka kai a gidan rawa a kasar Rasha a ranar Juma'a da daddare.

Akalla dai rayukan mutane 137 suka salwanta a lamarin da ya faru a birnin Moscow, yayin kuma da wasu 140 suka jikkata.

Firaministan kasar Faransa, Gabriel Attal shi ne ya sanar da kara matakan na ankararwa a kasar ta shafinsa na X.

Musamman dai firaministan na Faransa, ya ce kasar na maida hankali sosai a kan daukar alhakin harin na Rasha da kungiyar IS ta yi.

Sanarwar kuwa na zuwa ne, bayan ganawar gaggawa da Shugaba Emmanuel Macron na Faransar ya yi da mayan shugabannin tsaro na kasar.