Zaben Guinea ya bar baya da kura
March 26, 2020Yanzu haka dai hukumar zaben kasar ta Guinea Conakry ba ta bayyana sakamakon zaben 'yan majalisun dokoki da na kuri'ar raba gardama a kan kudin tsarin mulkin kasar da aka kada ba. An dai samu mummunan tashin hankali a yayin zabukan guda biyu da aka yi a lokaci guda, inda har aka samu asarar rayuka mutane kimanin 30. Ko da ya ke gwamnati ta ce mutum shida ne kawai suka mutu.
Aringizo da fasa akwatunan zabe
Rahotanni sun nunar da cewa an yi arginzon kuri'u yayin da a wasu mazabun aka fasa akwatunan zabe, abin da ya kusan janyo rikicin kabilanci a yankunan kurmi na kasar. An kone gidaje tare da kuma kashe wasu mutane, kamar yadda Fatou Blade wata mai fafutuka ta shaidar:
"Tun daga shekara ta 1958 ba mu taba ganin irin wannan zaben da ke cike tashin hankali ba, wanda aka kashe mutane da dama. Ina bakin ciki ba wai kawai a matsayina na 'yar fafutuka ba, amma a matsayina na 'yar kasa. Akwai takaici da bacin rai, haka kawai mutane su farma wadanda ba sa dauke da makamai, su kashesu kamar sun kashe kwari."
Tuni dai da Faransa ta ce ba ta amince da sakamakon zaben ba, abin da Fatou Balde ta bayyana da matsayin da ya dace, tana mai cewa kasar ta Guinea za ta ga sakamakon matakin na Faransa.
Zaton kawo gyara da sauyi
Farfese Alpha Condé na daya daga cikin tsofaffin manyan 'yan boko na Afirka da ya zauna a Faransa, inda ya dade yana gudun hijira tun lokacin mulkin kama karya na Sekou Turai. Ya yi ta fama na ganin samun sauyi na demokaradiyya a Guinea an kasance cike da fata da sa ran samun sauyi bayan da ya dare kan karagar mulki a shekara ta 2010.