1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Corona na kara bunkasa a Faransa

November 12, 2020

Faransa ta zama kasar da coronavirus tafi yawa a yanzu a nahiyar Turai. A ranar Laraba kimanin mutane 35,800 ne suka kamu da cutar, a jimlace kuma Faransar nada mutum kusan miliyan biyu da corona ta kama.

Frankreich Präsident Macron | Rede an die Nation
Hoto: David Niviere/abaca/picture alliance

Kungiyar agaji ta  Doctors Without Borders ta ce tana duba yiwuwar daukar karin ma'aikata a kasar domin taimaka wa musamman a gidajen kula da tsofaffi, inda nan ne ake zullumin coronar za ta fi yin illa. Wannan na zuwa ne yayin da a Alhamis din nan cibiyar Robert Koch Institute mai kula da alkaluman corona a Jamus ta ce annobar ta fara raguwa a kasar. A cewar Lothar Wiele wani jami'i a cibiyar ya ce yanzu lambar yada cutar ta koma kasa da maki daya a maimakon maki daya da ake zullumin idan akwai shi cutar ta corona na ninkawa ke nan. Sai dai duk da wannan kwarin gwiwar mutum kusan 22,000 ne suka kamu da cutar ta corona a Jamus a ranar Laraba.