Faransa: Za a ci gaba da yarjejeniyar Iran
May 9, 2018Kakakin majalisar Ali Larijani ya ce matakin babban barazana ce ga tsaro da ma zaman lafiya ya kuma baiyana shakku kan alkawarin da sauran kasashen da aka kulla yarjejeniya da su suka dauka na mutuntata.
Tuni kasashen duniya suka fara mayar da martani kan ficewar Donald Trump daga yarjejeniyar, inda ministan harkokin wajen Faransa, Jean Yves Le Drian ya ce, ficewar Amirka bai sa yarjejeniyar ta mutu ba, ya kara da cewa kasashen Turai na shirin ci gaba da wannan yarjejeniyar inda ya ce za'ayi taron gaggawa a tsakanin ministocin harkokin wajen Jamus, da Birtaniya da Faransa da kuma takwaransu Iran a wannan Litinin mai zuwa. A yammancin jiya Talata ne shugaba Trump ya sanar da soke yarjejeniyar da kuma yin alkwarin kakkaba ma Iran sabbin takunkumi.