Faransa za ta agazawa Ukraine da daruruwan tankokin yaki
March 31, 2024![](https://static.dw.com/image/68283166_800.webp)
Ministan harkokin tsaron Faransa Sébastien Lecornu, ya ce kasarsa za ta tallafawa Ukraine da daruruwan tankokin yaki don kare kanta daga mamayar da Rasha ke mata, a daidai lokacin da aka shiga shekaru ta 3 da fara yakin.
Karin bayani:Shugaba Putin na Rasha ya ce akwai yiwuwar yakin duniya na uku
Mr Lecornu ya ce za a fara kai agajin motocin yakin ne a farkon shekara mai kamawa, tare da makamai masu linzami da ke kakkabo jiragen yaki na sama, da dai sauran makaman yaki.
Karin bayani:Jamus da Faransa da Poland sun tabbatar da shirin taimakon Ukraine
Makaman da Faransar za ta aikewa Ukraine dai tsoffi ne da aka samar da su tun a shekarar 1979, a kokarin da take na kawar da tsoffi tare da kera sabbi, in ji ministan tsaron na Faransa Sébastien Lecornu.