Isra'ila na shirin tsinke hulda da Faransa saboda Falasdinu
July 25, 2025
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce,ya yi ammanar cewa,amincewa da Kasar Falasdinu ,shi ne mataki mafi tabbas na samar da dauwammamen zaman lafiya a Yankin Gabas ta Tsakiya da ya jima yana fama da tashe-tashen hankula, da tushensu shi ne kunnan kashin da Isra'ila ke ci gaba da yi da amincewa da kafuwar Kasar Falalasdinu.
Tuni dai firaminstan Isra,ila Benjamin Natenyahu ya bayyana matakin da yi wa 'yan ta'dda tukuici.
Wanda ya ce aminta da kafuwar Falalsdinu tamkar ba su tukuici ne kan ayyukan ta'addanci.
Shi kuwa ministan cikin gidan Isra'ila mai matsanancin ra'ayin rikau Ben Gvir kira ya yi da kasar sa ta katse alaka da Faransa,muddin ta kuskura ta aikata abin da ya kira kuskuren da ba za su taba yafe mata ba:
''Idan har ta kuskura ta tafka wannan mummunan kuskuren, to babu ta yadda za ai yi mu yafe musu,sai dai kawai mu raba gari da kasar da tarihinta ke cike da zubar da jinin al,umomin da ta yi wa mulkin mallaka da wawushe musu dukiyoyinsu.''
Ita mai dai Amurka a ta bakin sakatarenta, Marco Rubbio ya bayyana matakin na Faransa da rashin tunani da lura da halin da ake ciki, yana mai jaddada cewa,ya yi amamnar cewa irin wannan matakin babu abun da zai tsinana sai rura wutar rikicin a maimakon kasheta.
A akasin haka,firaministan Kasar Spain Pedro Sanchez,wanda dama kasar sa ta jima da aminta da Kasar Falalsdinu,ya yi maraba da matakin na Faransa,yana mai kira ga sauran kasashen Turai da su gaggauta bin sawunta.
Shi kuwa shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan,,siffanta matakin ya yi, da wata manuniya kan yadda duniya ke ci gaba da mayar da Isra'ila saniyar ware a duniya sakamakon mulkin wariya da mamayar da take wa Falalsdinu.
A yayin da kungiyar kasashen Larabawa ta bayyana matakin da mai karfafa guiwa ga Falalsdinawa a fafutukar neman 'yancin da suka jima suna yi.