1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa za ta bai wa Ukraine wani tallafi

January 5, 2023

Yayin da Ukraine ke fama da yaki da Rasha takaddamar a kanta a bara, Faransa ta ce za ta aika mata da wasu sabbin motocin sulke domin ta kare kanta.

Tankin yaki samfurin AMX-10 RC daga Faransa
Hoto: Emmanuel Dunand/AFP

Tallafin motocin na yaki dai ya biyo wata tattaunawa ce ta waya da ta gudana tsakanin shugaban Faransa Emmanuel Macron da na kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy.

Wannan ne karo na farko da za a aika da irin wannan samfuri na motocin sulke da aka kera a yammacin duniya.

Ba a dai bayyana adadin motocin ko ma sanar da cikakken lokaci da za su isa Ukraine din ba ya zuwa wannan lokaci.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine, ya yi godiya ga Faransa.

Kafin yanzu dai Faransar ta mika wa Ukraine din wasu manyan makaman kakkabe hare-haren makaman atilare da na masu linzami.