1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Faransa za ta ciwo bashin da bata taba cin irinsa ba

September 29, 2026

Matakin na zuwa ne a lokacin da ake sukar gwamnatin Macron da kashe kudi wajen gudanar da mulki.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel MacronHoto: Thomas Samson/AFP

Faransa ta bayyana cewa tana shirin karbar rancen da ya fi kowanne yawa a shekara mai zuwa.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yawan kusin da ake kashewa wajen gudanar da gwamnati.

Jamus ta soki Faransa da kin kashe kudin fannin tsaron Turai

Hukumar da ke kula da karbar bashi ta gwamnatin Faransa AFT, ta ce tana shirin karbar yuro biliyan €340 ($385bn) a shekarar 2027.

Wannan ya fi adadin da za ta karba a bana da kusan yuro biliyan 28, domin taimakawa wajen biyan kudaden gwamnati da kuma biyan wasu basussuka.

AFT ta bayyana hakan ne kwanaki biyu kafin gwamnati ta gabatar da kasafin kudin shekarar 2027.

Macron na jagorantar gangamin tallafawa Ukraine

Hukumar ta ce za ta fitar da takardun bashin gwamnati na matsakaici da na dogon lokaci domin samun kudin.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW