1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Faransa za ta dage dokar ta-baci a New Caledonia

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 27, 2024

A ranar 15 ga watan Mayun nan ne dai shugaba Macron ya sanya dokar tare da aikewa da 'yan sanda 380

Hoto: Ludovic Marin/Pool Photo via AP/picture alliance

Faransa za ta dage dokar ta-baci da ta sanya a kasar New Caledonia da ke karkashin ikonta, kwanaki 12 kenan bayan kakaba ta da fadar shugaba Emmanuel Macron ta yi, biyo bayan barkewar tarzoma.

Karin bayani:Igiyar ruwan tsunami a New Caledonia

A ranar 15 ga watan Mayun nan ne dai shugaba Macron ya sanya dokar tare da aikewa da 'yan sanda 380, inda adadin 'yan sanda Faransa da ke kasar ya kai 3,500, bayan da al'ummar kasar suka yi yunkurin bijerewa dokar Faransa da ta za ta bai 'yan asalin Faransa mazauna New Caledonia damar yin zabe da kuma tsayawa takara.

Karin bayani:Faransa na neman wasu mahara ruwa a jallo

To sai dai ko an janye dokar ta-bacin, filin jirgin saman Noumea babban birnin kasar zai ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa ranar 2 ga watan Yuni mai kamawa.

A makon da ya gabata ne shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci kasar, don kwantar da hankulan jama'a, bayan da tarzomar ta yi sanadiyyar mutuwar masu zanga-zanga 7 tare da kama daruruwansu.