Faransa za ta janye sojojinta daga Burkina Faso
November 21, 2022Gwamnatin kasar Faransa ta ce ba ta fidda tsammanin janye dakarunta da ke aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Burkina Faso ba.
Zanga-zangar nuna kin jinin sojojin Faransa musamman a yammacin Afirka dai na ci gaba da karuwa a baya-bayan nan.
Ministan tsaron Faransar, Sebastien Lecornu ya ce gwamnatin kasar na da abubuwan nazari kan kasancewar dakarunta a kasashen Afirka.
Sai dai ministan ya ce sojojin kasar da ke sansanin Sabre na Ouagadougou babban birnin kasar ta Burkina Faso, sun taka rawa a yaki da mayakan tarzoma a yankin Sahel.
To sai dai ana ci gaba da turje wa zaman sojojin a kasar saboda shekaru da suka kwashe ba tare da kawo karshen mayaka masu ikirarin jihadi ba.
Ko a ranar Juma'ar da ta gabata ma dai sai da 'yan sanda suka tarwatsa daruruwan 'yan kasar Burkina Fason da suka mamaye ofishin jakadancin kasar da ke birnin na Ougadougou.