1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniTurai

Faransa za ta kara da Potugal a mataki na gaba

Mouhamadou Awal Balarabe
July 2, 2024

Potugal ta sha bakar wahala wajen doke Sloveniya, yayin da Faransa da ta yi nasarar yin waje rod da Beljiyam. Wannan yana nufin cewar Potugal da Faransa za su kece raini a zagaye na gaba na daf da kusa da na karshe.

Faransa ta yi nasara a kan Beljiyam ba tare da bugewa ba
Faransa ta yi nasara a kan Beljiyam ba tare da bugewa baHoto: Leon Kuegeler/REUTERS

Faransa ta yi wa Beljiyam abin da za a iya kwatantawa da haduwa goma duka goma, saboda wannan shi ne karo na biyar a haduwa biyar da ta samu nasara a kan makwabciyarta a muhimman gasannin Turai da na duniya. Amma a farkon wasan, ba a samu wasu munanan farmaki daga abokan hamayyan na fil azan ba, duk da taurarin da suka mallaka irin su Kylian Mbappe a bangaren les Bleus na Faransa ko Romelu Lukaku a bangaren Les Diables Rouges ta Beljiyam.

'Yan wasan Faransa sun ta gwada sa' a ta hanyar buga kwallo da ka iya tada tsuntsaye har sau 16 ba tare da kwalliyarsu ta biya kudin sabulu ba. Ko da a bangaren Beljiyam ma, kwazo da 'yan wasa suka nuna bai taka kara ya karya ba idan aka yi la'akari da fansa da suke neman dauka a kan takwarorinsu na Faransa. Maimakon haka ma, dara ce ta ci gida inda dan wasan Beljiyam Jan Verthongen  ya jefa daya-dayan kwallo a ragarsu bisa kuskure a minti na 85 da fara wasa bayan da Randal Kolo Muani na Faransa ya kai raraka.

Faransa na bukatar kara shiri

Randal Kolo Muani ya ce dole Faransa ta zange dantse idan tana son ganin badiHoto: Carmen Jaspersen/REUTERS

Duk da cewar wannan ci daya mai ban haushi ya ba wa Faransa damar hayewa matakin daf da kusa da na karshe, amma har yanzu ba ta ci kwallo na kashin kanta ba tun bayan da aka fara gasar Euro 2024 inda abokan hamayya ke jefa wa kansu kwallo a raga ko a yi canjaras. Saboda haka ne dan wasanta  Kolo Muani ke ganin cewar akwai bukatar zagen dance idan Faransa na son ganin badi. Ya ce: "Mun yi matukar farin ciki da wannan nasarar da muka samu. Dole ne mu ci gaba da wasa a haka. Mun samu damammaki masu yawa, ko da yake ba mu yi nasarar sarrafa dukanin su yadda ya kamata ba. Akwai bukatar daukar lokaci da nitsuwa a lokacin sarrafa kwallo a mataki na karshe."

Ita Faransa za ta yi wasanta na gaba da Potugal a yammacin Juma'a a Hamburg. Wannan jadawalin ya samu ne bayan da  'yan wasan Portugal suka doke takwarorinsu na Sloveniya a bugun daga kai sai mai tsaron gida da ci 3-0. Duk da cewar Potugal ce ta mamaye wannan wasa da ya gudana a Frankfurt, amma masu tsaron gidan Potugl da Sloveniya ne suka baje kolinsu ta hanyar kawar da farmakin da abokan hamayya ke kai musu a tsawon mintuna 120 na wasa. Da farko, Jan oblak na Sloveniya ya cafke  bugun fenareti da shararren dan wasan Potugal Cristiano Ronaldo ya buda a minti na 106, yayin da mai tsaron gidan Potugal Diogo Costa ya yi nasarar kawar da farmakin da Benjamin Sesko ya kai masa a minti na karshe na wasan.

Costa na potugal ya nuna bajinta

Godiya ta ci gaba da tabbta ga golan na Potugal Diogo Costa da ya ci gaba da nuna halin dattaku inda ya kama bugun daga kai sai mai tsaron gida guda uku na 'yan wasan Sloveniya, lamarin da ya ba wa kungiyarsa damar tsallakewa zuwa zagaye na gaba, saboda nakaltar sirri abokan hammaya da Diogo Costa ya ce ya yi.

Diogo Costa na Potugl ya zama gwarzo bayan kama bugun fenarati huduHoto: Lars Baron/Getty Images

Ya ce: "Ba shakka na yi aiki sosai kuma na yi nazari salon bugun abokan hamayyarmu, amma na yi amfani da hankalina. Na yi imani da baiwata kuma bisa taimakon Allah na taimaka wa kungiyarta, wanda shi ne abu mafi muhimmanci a gare ni. Na yi farin ciki da samun damar hayewa. Ina fatan zan iya taimaka wa kungiyarmu a wasa na gaba."

Digo Costa na da shekaru 24 da haihuwa, kuma baya ga babbar kungiyar kwallon kafar Potugal yana bugawa a kungiyar Porto.