1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Faransa za ta rufe ofishin jakadancinta na Jamhuriyar Nijar

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 22, 2023

Za a sallami ma'aikatan jakadancin 'yan asalin Nijar daga ranar 30 ga watan Afrilun sabuwar shekara mai kamawa ta 2024

Hoto: AFP

Faransa za ta rufe ofishin jakadancinta na Jamhuriyar Nijar, biyo bayan tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi, wanda ya hambarar da gwamnatin Dimokuradiyya ta Mohamed Bazoum.

Karin bayani:Chadi ta amince da raka sojojin Faransa kan iyaka

Wannan na cikin wata wasika da aka aikawa ofishin jakadancin Faransa da ke Yamai babban birnin kasar mai dauke da kwanan watan 19 ga Disambar nan, wadda kuma kamfanin dillancin labarai na Associate Press ya yi tozali da ita, kuma majiyar ofishin ta tabbatar da sahihancinta.

Wasikar ta nuna cewa za a sallami ma'aikatan jakadancin 'yan asalin Jamhuriyar Nijar daga ranar 30 ga watan Afrilun sabuwar shekara mai kamawa ta 2024.

karin bayani:Fara janye dakarun Faransa

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wa'adin ficewar sojojin Faransa daga Nijar din ke cika.