Faransa za ta taimaki Najeriya don magance matsalolin tsaro
December 7, 2025
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya alkawarta tallafa wa Najeriya wajen magance matsalolin tsaron da suka addabe ta, kamar yadda shugaba Bola Tinubu ya nemi agaji, makonni bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin kutsa wa kasar domin kare kiristoci daga kisan kare dangi da ya yi zargin ana yi musu.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Mr Macron ya ce sun tattauna ta wayar tarho da Mr Tinubu ranar Lahadi, wanda ya mika kokon barar magance wa Najeriya kalubalen tsaro, musamman na yankin arewacin kasar.
Karin bayani:Mahawara mai zafi a kan ziyarar Tinubu a Paris
To sai dai shugaba Macron bai fayyace irin tallafin da zai bai wa Najeriya ba, a wannan lokaci da kasarsa ta janye dakarun sojinta daga yammaci da kuma tsakiyar Afirka, sakamakon tsamin danganta da kasashen da ta yi mulkin mallaka.