Faransa: Zagaye na biyu na zaben 'yan majalisar dokoki
July 7, 2024Talla
A wannan Lahadin Faransawa ke kada kuru'u a zagaye na biyu na zaben 'yan majalisar dokokin kasar wanda ake ganin zai iya samar da gwamnatin masu ra'ayin rikau tun bayan yakin duniya na biyu.
Karin bayani: Ana zaben 'yan majalisar dokoki a Faransa
Ana dai ganin ta yiwu jami'iyar masu kyamar baki ta Marine Le Pen, ta iya samun rinjaye a majalisar a karon farko. Idan har jam'iyyar ta National Rally ta lashe kujeru 289, ana sa ran Shugaba Emmanuel Macron ya nada shugaban jam'iyyar a matsayin sabon Firanministan kasar. Sai dai kuma babu tabbaci kan yadda sakamakon zai kasance saboda tsarin zaben da kuma yadda dukannin jam'iyyun suka dau damara.