Faransawa ba sa son yaki a Mali
January 12, 2021Talla
Binciken cibiyar IFOP da aka wallafa a mujallar Le Point ya nuna cewa kaso 51,% na al'ummar Faransa basa son ci gaba da yaki da 'yan ta'adda a Mali, adadin da ya kasance mafi rinjaye idan aka kwatanta da wadanda suka nuna amincewarsu lokacin da Faransa ta shiga yaki da 'yan ta'adda a Mali a shekarar 2013.
Wannan lamarin na zuwa ne bayan wasu hare-haren ta'addanci biyu da suka hallaka sojojin Faransa biyar a farkon watan Janairun 2021 a Mali.